IQNA

Zanga-Zangar Allawadai Da Barazanar Kone Kur'ani A Afghanistan

15:01 - September 12, 2010
Lambar Labari: 1991956
Bangaren siyasa da zamantakewa; Wasu musulmi sun gudanar da zanga-zanga a jiya a Afghanistan domin yin Allawadai da barazanar kone kur'ani mai tsarki da wani mai kiran kansa malamin addinin kirista ya yi a kasar Amurka.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga wani shafin sadarwa na yanar gizo an habarta cewa, Wasu kungiyoyin musulmi sun gudanar da wata gagarumar zanga-zanga a jiya a kasar Afghanistan domin yin Allawadai da barazanar kone kur'ani mai tsarki da wani mai kiran kansa malamin addinin kirista ya yi a jahar Florida.

Wadanda suka gudanar da zanga-zangar yin ta la'antar mutumin da ya yi wannan barazana, tare da bayyana hakan a matsayin dabbanci da kuma rashin sanin addinin Musulunci da hakikanin koyarwarsa.

Wasu daga cikin wadanda suka gudanar da zanga-zangar sun samu raunuka sakamakon ba ta kashi da suka yi da jami'an tsaron kasar, wadanda suka afka kan masu gudanar da jerin gwanon.

652332
captcha