Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a daidai lokacin yake mika sakon murnar idin karamar salla ga al'auumar kasarsa, Shugaban kasar Indonesia ya yi kira ga dukkanin cibiyoyin addini na kasar Amurka da su nuna rashin amincewarsu da barazanar kone kur'ani da wani malamin addini kirista da wasu 'yan tsirarun mabiyansa ke hankoro.
A wani rahoton da jaridar darul khalij ta buga, an bayyana cewa shugaban na Indonesia ya gargadi malamin addinin kiristan na kasar Amurka da kada wani gigi ya kai shi har yak one kur'ani, domin kuwa abin da zai biyo baya ba zai yi wa kowa dadi a duniya ba.
652357