IQNA

Shugaban Labanan Ya Kalubalanci Masu Niyar Kone Kur'ani

16:11 - September 12, 2010
Lambar Labari: 1992056
Bangaren siyasa da zamantakewa, Shugaban kasar Labanan Michel Sulaiman ya bayyana cewa kira zuwa ga kone kur'ani mai tsarki ya hannun riga tunanin tattaunawa tsakanin mabiya addinai na duniya.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga bangaren yada labaransa na birnin Berut fadar mulkin kasar Labanan cewa, Shugaban kasar Michel Sulaiman ya bayyana cewa kira zuwa ga kone kur'ani mai tsarki ya hannun riga tunanin tattaunawa tsakanin mabiya addinai na duniya da ake yi.

Sulaiman ya bayyana hakan ne a cikin wani bayani da ya fitar da aka watsa jiya, dangane da barazanar da wani malamin addinin kirista na kasar Amurka ya yin a kone kur'ani a ranar tunawa da harin 11 ga watan Satumba.

Shugaban kasar ta Labanan ya yi Allawadai da wannan ikirari, tare da bayyana shi da cewa wannan ba mataki ne na hankali ko ilimi ba, ba kuma ko yi ne da addinin kiristanci ba.

652355


captcha