Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na kamfanin dillancin labaran Syria-news an habarta cewa, Babban limamin birnin Damascus na kasar Syria ya bayyana cewa addinin Musulunci addini ne na dukkanin al'ummomin duniya ba na wata al'umma kadai ba kamar yadda wasu suke zato.
Malamain ya bayyana hakan ne a cikin hudubar sallar idi da ya gabatar, inda ya jaddada cewa addinin muslunci addini ne da kowa zai iya amfana da koyarwarsa a cikin dukkanin sassa na rayuwa ta yau da kullum.
Ya kara da cewa ya zama wajibi musulmi su dauki lokuta masu albarka na idi domin tabbatar da hadin kai a tsakaninsu a fadin duniya.
652354