IQNA

Tsaurin Ra'ayi Na Barazana Ga Rayuwar Mabiya Addinai

16:13 - September 12, 2010
Lambar Labari: 1992062
Bangaren syasa da zamantakewa; Babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen musulmi Ihsan Oglo ya bayyana cewa barazanar kone kur'ani mai tsarki da wani kirista na kasar Amurka ya yi, hakan na yin barazana ga mabiya addinai.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani bayani day a nakalto daga shafin sadarwa na kungiyar OIC an habarta cewa, babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen musulmi Ihsan Oglo ya bayyana cewa barazanar kone kur'ani mai tsarki da wani mai kiran kansa malaman addinin kirista na kasar Amurka ya yi, hakan na yin barazana ga mabiya addinai a sassa daban-daban na duniya.

Ya ce dole ne mutane su san cewa abin da wannan mutum ke ikirarin zai zai yi barazana ce ga dukkkanin maiya addinai a duk inda suke a duniya, akan dole ne ma'abuta hankali da hukumomi su safke nauyin da ya rataya kansu.

652349



captcha