IQNA

Mabiya Addinai A Amurka Sun Gudanar Da Karatun Kur'ani

8:51 - September 13, 2010
Lambar Labari: 1992178
Bangaren kasa da kasa; Mabiya addinai daban-daban a kasar Amurka sun gudanar da karatun kur'ani mai tsarki na bai daya domin kalubalantar kiristan da ke yin kira zuwa ga kone kur'ani mai tsarki.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na wral cewa, mabiya addinai daban-daban a kasar Amurka sun gudanar da karatun kur'ani mai tsarki na bai daya domin kalubalantar kiristan da ke yin kira zuwa ga kone kur'ani mai tsarki a ranar tunawa da harin 11 ga watan satumba.

Mabiya addinan sun gudanar da karatun kur'anin ne domin nuna goyon baya ga musulmi kan tsangwamar da suke fuskanta daga masu tsattsauran ra'ayin kiyayya da addinin Musulunci a kasar, musamman ma a cikin wannan lokaci.

Daga cikin mabiya addinan da suka halarci wurin sun hada da wakilan kungiyoyin kiristoci da majami'oi gami da kungiyoyin yahudawa masu kiyayya da akidar sahyuniyanci.

652567



captcha