Bangaren kasa da kasa; Kungiyar bunkasa harkokin ilimi da al'adun Musulunci ta ISESCO ta bukaci da a ladabtar da duk wasu masu hankoron wulakanta addinai a duniya, tare da samar da dokoki na kasa da kasa kan hakan.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga wani shafin sadarwa na yanar gizo cewa, kungiyar bunkasa harkokin ilimi da al'adun Musulunci ta ISESCO ta bukaci da a ladabtar da duk wasu masu hankoron wulakanta addinai a duniya, tare da samar da dokoki na kasa da kasa kan irin wannan mummunan laifi.
Kungiyar ta sanar da hakan ne a cikin wani bayani da ta fitar dangane da kiran da wani kirista a Amurka ya yi da ke neman a kone kur'ani a ranar tunawa da hare-haren 11 ga watan satumba da aka kai Amurka a cikin shekara ta 2002.
Bayanin ya ce dole a dauki kwararan matakai kan duk wani wanda ke da irin wannan mummunar manufa kan Musulunci, domin kuwa irin wannan tunani kansa barazana ne ga zaman lafiyar duniya.
652518