Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, wani rahoto da jaridar kasar Qaatr ta buga mai suna al-raya ya yi nuni da cewa, bayan da kiristan nan mai tsananin gaba da addinin Musulunci a Amurka ya janye daga batun kone kur'ani mai tsarki da sanar cewa zai yi a ranar 11 ga watan satumba, wasu daga cikin majami'oin Amurka sun kudiri aniyar aiwatar da abin da ya yi niyya kuma ya fasa.
Majami'oin da suka dauki wannan kudiri n daga cikin wadanda suka shahara da kiyayya da addinin muslunci, kamar yadda bas u amince da koyarwar addinin kiristanci kan lamurra da dama ba, musamamn inda yak e yin kira zuwa ga zaman lafiya da fahimtar juna tare da sauran addinai.
652639