IQNA

Taro Kan Tasirin Addini A Dabi'u Na Zamantakewa A Faransa

8:53 - September 13, 2010
Lambar Labari: 1992185
Bangaren kasa da kasa; Za a gudanar da wani zaman taro a kasar faransa kan tasirin addini a cikin rayuwa da kuma dabiun mutane da suka shafi rayuwarsu ta zamnatakewa a kasar faransa.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin yanar gizo na calenda cewa, za a gudanar da wani zaman taro a kasar faransa kan tasirin addini a cikin rayuwa da kuma dabiun mutane da suka shafi rayuwarsu ta zamnatakewa a kasar faransa, wanda kungiyar kula da harkokin addini ta kasar ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa.

A wajen taron za a gabatar da laccoci da kuma makaloli wanda masana daga sassa daban-daban na kasar za su gabatar, da suka hada da malaman addinin muslunci da kuma malaman addinin kirista.

Babbar manufar gudanar da taron dai ita ce kara fadakar da matasa kan muhimmancin sanin addinin, da kuma fahimtar rayuwa ta zamantakewa a koyar addinai, tare da zama lafiya da juna.

652700


captcha