Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na jaridar kasar Masar ta yaum sabi an bayyana cewa, majami'oin kasar da suka hada dukkanin darikokin mabiya addinin kirista sun yi Allawadai da matakin kone kur'ani da wasu masu kiran kansu kirista suka yi a kasar Amurka da nufin cin zarafin musulmi.
Majami'oin sun bayyana hakan ne a cikin wani bayani da suka fitar na bai daya, da ke cewa nuna kiyayya ga musulmi da addinin Musulunci ba ya cikin akida ta addinin kirista, bil hasali ma hakan ya yi hannun riga da akidar wannan addini da koyarwarsa.
Haka nan kuma bayanin ya tabbatar da cewa dukkanin wadanda suka aikata wannan mummunan aiki ba su da wata masaniya kan addinin kirista, kuma ba wakiltarsa.
653503