IQNA

Musulmi A Amurka Sun Bukaci A Hukunta Masu Wulakanta Kur'ani

12:20 - September 14, 2010
Lambar Labari: 1993543
Bangaren kasa da kasa; Wasu daga cikin jagororin musulmi a kasar Amurka sun bukaci da a gurfanar da duk wadanda suke da hannu wajen kone kur'ani mai tsarki da aka yi a kasar a gaban kuliya domin fuskantar shari'a.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na detnews an habarta cewa, wasu daga cikin jagororin musulmi a kasar Amurka sun bukaci da a gurfanar da duk wadanda suke da hannu wajen kone kur'ani mai tsarki da aka yi a kasar a gaban kuliya domin fuskantar shari'a kan danyen aikinsu.

Musulmin sun sanar da hakan ne bayan da wasu tsagera akasar Amurka suka dauki matakin kone kur'ani mai tsarki, sakamakon janyewar da mutumin na farko ya yi wanda ya fara yin barazanar kone kur'ani, amma bayan nuna fushin da musulmi suka yi ya janye.

Yanzu haka dai gwamnatin Amurka ba ta nuna wata damuwa kan cin mutuncin abubuwa masu tsarki na musulmi da ake yi a cikin kasarta ba, illa bayyana hakan da cewa zai jefa sojojinta cikin hadari a Afghanistan.

653614



captcha