IQNA

Musulmi Da Kirista A Amurka Sun Gudanar Da Karatun Kur'ani

12:12 - September 14, 2010
Lambar Labari: 1993544
Bangaen kasa da kasa; Dubban musulmi da kiristoci ne suka taro a wata cibiya domin gudanar da karatun kur'ani mai tsarki na bai daya, domin tabbatar da hadin kai da fahimtar juna a tsakaninsu, da kuma barranta daga masu wulakanta kur'ani.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na wcco an bayyana cewa, dubban musulmi da kiristoci ne suka taro a wata cibiya domin gudanar da karatun kur'ani mai tsarki na bai daya, domin tabbatar da hadin kai da fahimtar juna a tsakaninsu, da kuma barranta daga masu wulakanta kur'ani a cikin kasar.

An gudanar da wannan taro ne a cikin birnin Jaska na kasar ta Amurka, inda dukkanin mutanen da suka halrci da suka hada da kiristoci da musulmi har ma da yahudawa suka yi allawadai da wanmann mummnuan aiki, tare da bayyana shi da cewa aiki ne na marassa addini.

653945


captcha