Bangaren kasa da kasa; Za a gudanar da wani zaman taro tsakanin musulmi da kiristocin kasar Iran a lardin Azarbaijan ta gabas, wanda kungiyar tattauwa tsakanin addinai ta kasar Iran ta shirya gudanarwa.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, za a gudanar da wani zaman taro tsakanin musulmi da kiristocin kasar Iran a lardin Azarbaijan ta gabas, wanda kungiyar tattauwa tsakanin addinai ta kasar Iran ta shirya gudanarwa wanda zai samu halartar shugaban kwamitin tattaunawar addinai ta duniya.
Bayanin ya ci gaba da cewa bababr manufar gudanar da wannan zaman taro ita ce kara tabbatar da hadin kai da fahimtar juna tsakanin mabiya addinan biyu, tare da yin Allawadai da kone ku'ani mai tsarki da wasu kiristoci suka yi a kasar Amurka.
654270