Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani bayani da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, daya daga cikin 'yan majalisar dokokin Amurka ya bayyana cewa mafi yawan Amurkawa ba su da wata masaniya kan addinin Musulunci ballantana har su kare shi.
Dan majalisar wanda kan dage wajen kare hakkokin musulmi a majalisar dokokin Amurka ya bayyana cewa, babu wani dalili da zai sanya a tsani musulmi, domin kuwa su ma mabiya addini ne kamar yadda kiristoci suke bin addininsu.
Ya ce suna da hakin su gina masallatai da wuraren tarukan addininsu, kamar yadda kiristoci suke da hakkin gina nasu wuraren addini.
654454