Bangaren kasa da kasa; Kungiyar bunkasa harkokin ilimi da al'adun kasashen mulmi za ta halarci taron kasa da kasa kan tattaunawar addinai tsakanin al'ummomin duniya, da za a gudanar a kasar Switzerland.
Kamfanin dillancin labaran kur'ani mai tsaki na Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga bangaren hulda da jama'a na ISESCO cewa, kungiyar bunkasa harkokin ilimi da al'adun kasashen mulmi za ta halarci taron kasa da kasa kan tattaunawar addinai tsakanin al'ummomin duniya, da za a gudanar a kasar Switzerland a nan gaba.
Wannan zaman taro zai samu halartar wakilai daga kasashe duniya daban-daban da suka hada da na musulmi da na larabawa, domin tattaunawa muhimman lamurra da suke da dangantaka da harkokin ilimi na kasashen duniya.
An kafa wannan kungiya tun a cikin shekara ta 1986, da nufin samar da wata hanya ta hada kan al'ummomin duniya da bunkasa harkokin ilimi da al'adunsu.
655331