IQNA

Za A Gudanar Da Baje Kolin Kayayyakin Tarihin Mulunci A Jamus

16:32 - September 16, 2010
Lambar Labari: 1995220
Bangaren kasa da kasa; Za agudanar da wani taron baje koli na kayyakin Musulunci da kuma kayan tarihin addinin Musulunci a birnin Munikh na kasar Jamus, tare da halartar wakilan kungiyoyin musulmi daban-daban.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani bayani da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na hurriyet an bayyana cewa, za agudanar da wani taron baje koli na kayyakin Musulunci da kuma kayan tarihin addinin Musulunci a birnin Munikh na kasar Jamus, tare da halartar wakilan kungiyoyin musulmi daban-daban a kasar.

Bayanin ya ci gaba da cewa wannan baje koli zai hada da kayyakin tarihin musulmi da kuma wasu daga cikin hotunan wurare masu tsarki a cikin addinin muslunci gami da takaitaccen tarihinsu.

Babbar manufar gudanar da wannan taron baje koli ita ce kara wayar da kan mutanen kasar da suke da karancin masaniya kan addinin Musulunci da tarihinsa.

655413




captcha