Bangaren kasa da kasa; Za a gudanar da wani zaman taro a kasar Morocco da zai dubi kan tsarin ilimi a mahangar kur'ani mai tsarki, da kuma yadda kasashen musulmi za su iya yin amfani da shi a acikin manhajojin karatun makaratunsu.
Kamfanin dilalncin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa, a wani bayani da ya nakalto daga shafin sadarwa na map an bayyana cewa, za a gudanar da wani zaman taro a kasar Morocco da zai dubi kan tsarin ilimi a mahangar kur'ani mai tsarki, da kuma yadda kasashen musulmi za su iya yin amfani da shi a acikin manhajojin karatun makaratunsu na firamare da kuma sakandare.
Ma'aikatar ilimi ta kasar ce tare da hadin gwiwa da ma;ikatar kula da harkokin addini ta kasar Morocco ne suka shirya gudanar da wannanzaman taro, da nufin habbaka koyarwa bisa mahangar addinin a cikin makarantun kasar.
Bayanin ya kara da cewa taron zai samu halartar manyan jami'ai daga sassa daban-daban na maikatun kasar, kamar yadda zai samu halartar baki daga waje da aka aikewa goron gayyata.
655493