IQNA

Taron Ministocin Harkokin Ilmi Na Kasashen Musulmi A Malazia

16:31 - September 16, 2010
Lambar Labari: 1995222
Bangaren kasa da kasa; Za a fara gudanar da wani taro na kasa da kasa na ministocin harkokin ilimi mai zurfi na kasashen musulmi a birnin Kualalampour fadar mulkin kasar Malazia.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na icmhers cewa, za a fara gudanar da wani taro na kasa da kasa a Malazia, na ministocin harkokin ilimi mai zurfi na kasashen musulmi a birnin Kualalampour fadar mulkin kasar.

Bayanin ya kara da cewa ma'aikatar kula da harkokin ilimi mai zurfi ta kasar Malazia ita ce ta dauki nauyin bakuncin taron, wanda na kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC ta shiya tare da sa idon kungiyar bunkasa harkokin ilimi da al'adun kasashen musulmi ISESCO.

Wannan dai shi ne karo na biyar da za a gudanar da irin wannan taro a matsayi na kasa da kasa, kuma an shirya gudanar da shi a cikin 'yan kwanaki masu zuwa.

655440




captcha