IQNA

Wasu Yahudawan Sahyuniya Sun Keta Kur'ani A Birnin Qods

16:30 - September 16, 2010
Lambar Labari: 1995224
Bangaren kasa da kasa; A daidai lokacin da al'ummar musuolmi sanma da bilyan daya da rabi a fadin duniya suke ta nuna rashen amincewa da kone kur'ani da wasu suka yi a Amurka, wasu yahudawan sahyuniya sun keta kur'ani mai tsarki a birnin Qods.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani bayani da ya nakalto daga shafin sadarwa na bna an habrta cewa, daidai lokacin da al'ummar musuolmi sanma da bilyan daya da rabi a fadin duniya suke ta nuna rashen amincewa da kone kur'ani mai tsarki wasu kiristoci suka yi a Amurka, wasu tsirarun yahudawan sahyuniya su ma sun keta kur'ani mai tsarki a birnin Qods mai alfarma.

Bayanin ya ci gaba da cewa yahudawa sun aikata hakan ne bisa cikakken goyon bayan da suke samu daga gwamnatocin Amurka da wasu kasashen yamamcin turai, wadanda suke cin karensu babu babbaka kan addinin Musulunci da sunnan 'yancin ra'ayi.

655749




captcha