Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na kamfanin dillancin labaran jihan cewa, Mabiyar mazhabar shi'a a kasar Turkiya sun yi kakkausar suka da yin Allawadai da tozarta kur'ani mai tsarki da wasu tsirarun kiristocin sahyuniya suka yi a kasar Amurka.
Bayanin ya ci gaba da cewa shugaban kwamitin kula da harkokin mabiya mazhabar iyalan gidan manzon Allah a kasar Turkiya ya fitar da wani bayani da a cikinsa aka yi allawadai da cin zarafin musulmi da keta alfarmar kur'ani mai tsarki.
Ya kara da cewa a cikin bayanin a madadin dukkanin mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah na kasar, yana kira ga dukkain musulmi da su kalubalanci irin wannan mataki na cin zarafin addinin Musulunci.
656546