IQNA

Shugaban OIC Ya Bukaci A Taimaka Ma Al'ummar Pakistan

10:01 - September 18, 2010
Lambar Labari: 1995713
Bangaren kasa da kasa; Shugaban kasar Senegal Abdullah Wad ya kirayi al'ummar musulmi daga ko'ina cikin fadin duniya da su taimaka ma 'yan uwansu da ambaliyar ruwa ta yi wa yankan kauna a kasar Pakistan.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo afriqueactu cewa, Shugaban kasar Senegal Abdullah Wad ya kirayi al'ummar musulmi daga ko'ina cikin fadin duniya da su taimaka ma 'yan uwansu da ambaliyar ruwa ta yi wa yankan kauna a kasar Pakistan a cikin 'yan lokutan nan.

Abdullah Wad ya bayyana hakan ne a cikin wani bayani da ya fitar, inda ya bayyana cewa; Ina kira ga dukkanin gwamnatoci na kasashen musulmi, da kungiyoyin musulmi da kwamitoci da su taka rawa wajen hada taimako ga mutanen Pakistan da suke cikin mawuyacin hali sakamakon ambaliyar ruwa.

Ya ce babu wani abin da za mu iya yi wajen hana faruwar bala'oi na dabi'a, amma za mu iya taimaka wad a dukaknin abin da Allah ya hore mana domin agazawa wadanda abin ya rutsa da su.

656590


captcha