IQNA

An Gudanar Da Addu'ar Du'aul Komail A Faransa

12:31 - September 18, 2010
Lambar Labari: 1995926
Bangaren kasa da kasa; An gudanar da addu'ar du'aul komail a kasar Faransa kamar yadda aka saba gusdanarwa adaren kowace ranar juma'a a birnin paris fadar mulkin kasar.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani bayani da ya samu daga bangaren hulda da jama'a na cibiyar bunkasa ayyukan Musulunci ta Zahra (AS) da ke kasar faransa an bayyana cewa, An gudanar da addu'ar du'aul komail a kasar Faransa kamar yadda aka saba gusdanarwa adaren kowace ranar juma'a a birnin paris.

Bayanin ya ce wannan karon taron du'aul Komail da aka gudanar a babban ginin cibiyar da ke cikin birnin paris ya samu halartar Iraniyawa da dama mazauna birnin, da suka hada da ma'aikata da kuma dalibai.

Karatun du'aul komail na daya daga cikin taruka na mako-mako da wannan cibiya kan dauki nauyin gudanarwa, tare da halartar musulmi.

656550





captcha