IQNA

An Saka Darussan Musulunci A Cikin Tsarin Karatu A Jamus

12:32 - September 18, 2010
Lambar Labari: 1995928
Bangaren kasa da kasa; Babban kwamishin mai kula da ayyukan ma'aikatar raya a'adu ta jahar Niedersachsen ya bayyana cewa, an saka darussan Musulunci a cikin tsarin karatun wannan jaha, da zai fara aiki daga shekara ta 2012.



Kamfanin dillancin labaran kur'ani mai tsarki na iqna ya habarta cewa, babban kwamishin mai kula da ayyukan ma'aikatar raya a'adu ta jahar Niedersachsen ya bayyana cewa, an saka darussan Musulunci a cikin tsarin karatun wannan jaha, da zai fara aiki daga shekara ta 2012 a dukkanin makarantun sakandare na jahar.

Ya ce ya zuwa yanzu an fara aikwatar da wannan shiri a matsayin gwaji a wasu makarantun sakandare 42 da ke cikin jahar, kuma kimanin dalibai dubu biyu ne suka fara koyon wani abu daga darussan addinin Musulunci.

Bisa jawabin nasa, da zaran an samu malamai da za su iya koyar da darussan addinin muslunci a makarntun sakandare na jahar, za a fara aiki da tsarin gadan-gadan a cikin shekara ta 2012 idan Allah ya kaimu.

656618




captcha