IQNA

Za A Gudanar Da Gasar Kur'ani Ta Matasa Larabawa A UAE

12:32 - September 18, 2010
Lambar Labari: 1995939
Bangaren kasa da kasa; Za a gudanar da gasar karatu da hardar kur'ani mai tsarki ta matasa larabawa da ke cikin kasashe mambobi a kungiyar daulolin larabawan tekun fasha, wadda za a fara gudanarwa daga gobe Lahadi.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da ya nakallto daga kamfanin dillancin labaran wam na kasar hadaddiyar daular larabawa an bayyana cewa, Za a gudanar da gasar karatu da hardar kur'ani mai tsarki ta matasa larabawa da ke cikin kasashe mambobi a kungiyar daulolin larabawan tekun fasha, wadda za a fara gudanarwa daga gobe.

Wannan gasa za ta samu halartar matasa daga sassa daban-daban na kasashen larabawa mambobin a kungiyar hadin gwiwa ta larabawa tekun fasha, wadda za a gudanar a birnin Dubai cibiyar kasuwancin kasar.

Gasar za ta mayar da hanakali ne kan karatu da kuma harda, inda za a kasa bangarorin da za a gudanar da ita domin bayar da dama ga masu shiga su zabi bangaren da suke so.

656812





captcha