Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na zainabiyya cewa, kwamitin koli na malaman mazhabar iyalan gidan manzon Allah a kasar Turkiya ya yi Allawadai da keta alfarmar kur'ani mai tsarki da wasu marassa addini suka yi a kasar Amurka a cikin makon da ya gabata da nufin tozarta musulmi.
A cikin wani da kwamitin ya fitar ya bayyana cewa, a koda yaushe musulmi suna fuskantar tsokana daga wasu masu neman tashin hankali da mayar da duniya cikin rudani, amma musulmi suna kawar da kai daga hakan.
Bayanin ya ce saboda hakurin musulmi kan cin zarafin da ake yi musu a turai wannan har ya kai ga kone kur'ani littafi mai tsarki a Amurka, wanda hakan shi ne mummunan aiki irinsa na farko da duniya ta gani.
656932