Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga jaridar Al-raya ta kasar Qatar an bayyana cewa, an fara rijistan sunayen mutanen da suke samun horo kan ilmomin addini da na kur'ani a babbar cibiyar Nur ta kur'ani da ke birnin Doha fadar mulkin kasar.
Rahoton ya ce wannan shiri na bayar da horo ga masu sha'awar koyon ilmomin addini ana gudanar da shi har tsawon shekaru biyu, inda daga karshe za a bayar da takardun shedar kammar samun horo a wannan cibiya.
Daga cikin abubuwan da ake bayar da horo kansu har da ilmomin kur'ani, hadisi, tajwidi, fikihu harshen larabci da dai sauransu. Da kuma karatun kur'ani gami da harda.
657013