Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani bayani da ya naklato daga shafin sadarwa na shugaban kasar Iran an bayyana cewa, Shugabannin kasashen Iran da Syria sun gudanar da zaman tattaunawa na musamamn kan lamurra da dama da suka danganci duniyar musulmi da sanin yadda ya kamata a magance su a tasakaninsu.
Wannan bayani ya yi ishara da cewa dukkanin shugabannin biyu suna da mahanga da ta yi kama da ta juna kan batun warware matsaloli da dama da suka addabi duniyar musulmi, musamman ma kan batun tsaro a yankin gabas ta tsakiya.
Dukkanin shugabannin biyu sun jadda wajabcin ci gaba da kara zurfafa dangantakarsu a dukkanin bangarori, musamman ma bangaren bunksa harkoki na tattalin arziki, da siyasa gami da tsaro.
656965