IQNA

Sayyid Nasrallah Ya Gana Da Shugaban Jami'ar Al-Mostafa (SAW)

12:07 - September 19, 2010
Lambar Labari: 1996779
Bangaren siyasa da zamnatakewa; Babban sakataren kungiyar gwagwarmaya ta hizbullah Sayyid Hassan Nasrullah ya gana da shugaban jami'ar Al-mostafa (SAW) dokta Alireza A'arafi a birnin Beirut.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga reshensa na kasar Labanan an bayyana cewa, babban sakataren kungiyar gwagwarmaya ta hizbullah Sayyid Hassan Nasrullah ya gana da shugaban jami'ar Al-mostafa (SAW) dokta Alireza A'arafi.

Bayanin ya yi nuni da cewa Sayyid Nasrullah tare da A'arafi sun tattauna kan muhimamn batutuwa da suka shafi batutuwa na ilimi da kuma al'adu da suka danganci kasashen musulmi, da yadda musulmi suke fuskantar kalu bale a wannan bangare.

Haka nan kuma sun batun cin zarafin da musulmi suke fuskanta daga al'ummomin kasashen turai ta hanayar wulakanta ababe masu tsarki a cikin addinin Musulunci, na baya-bayan nan shi ne keta alfarmar kur'ani mai tsarki.

656841





captcha