IQNA

Kone Kur'ani Ya Saba Wa Koyarwar Addinin Kiristanci

12:09 - September 19, 2010
Lambar Labari: 1996784
Bangaren kasa da kasa; Wasu daga cikin manyan malaman addinin kirista a kasar Iraki sun yi Allawadai da kone kur'ani mai tsarki, tare da bayyana hakan da cewa ya saba wa dukkanin koyarwar addinin kiristanci.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na jaridar Qods Al-arabi da ke bugawa a birnin London cewa, wasu daga cikin manyan malaman addinin kirista a kasar Iraki sun yi Allawadai da kone kur'ani mai tsarki, tare da bayyana hakan da cewa ya saba wa dukkanin koyarwar addinin kiristanci ga baki daya.

Bayanin ya ci gaba da cewa limamin majami'ar birnin Bagadaza Mikharl Sabah ya bayyana cewa kiristoci suna yin Allawadai da abin da suka yi da sunan kiristanci na kone kur'ani mai tsarki, kuma wadanda suka yi hakan su san cew ba su wakiltar kiristoci.

Shi ma a nasa bangaren William George limamin mabiya addinin kirista akasar Iraki ya bayyana cewa, wadanda suka kai harin 11 ga watan satumba masu tsatsauran ra'ayi ne daga cikin musulmi amma abin da suka yi ba Musulunci ba ne.

656864



captcha