Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga jaridar kasar Kuwait ta Alkabs an bayyana cewa, daya daga cikin mambobin kwamitin zartarwa na gamayyar kamfanonin kasashen musulmi ya bukaci da a kafa wani kwamiti da zai kula da harkokin saka hannayen jari a kamfanonin kasashen musulmi na duniya.
Bayanin ya ci gaba da cewa samar da irin wannan kwamitin na da matukar muhimmanci wajen samar da hanyar karfafa tattalin arzikin musulmi, musamman ma kasashe marrasa galihu daga cikinsu.
Gamayyar kamfanonin kasashen musulmi na taka gagarumar rawa wajen taimaka kamfanoni a kasashen musulmi masu bukatar taimako.
657822