IQNA

Taro Kan Allamah Abduh Da Allamah Mozaffar A Tehran

15:05 - September 20, 2010
Lambar Labari: 1997811
Bangaren kasa da kasa; Za a gudanar da zaman taro kan manyan malaman addinin msulunci Allamah Abduh da Allamah Mozaffar a birnin Tehran na jamhuriyar Musulunci ta Iran, tare da halar masana.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Za a gudanar da zaman taro kan manyan malaman addinin msulunci Allamah Abduh da Allamah Mozaffar a birnin Tehran na jamhuriyar Musulunci ta Iran, tare da halar masana daga kasashen musulmi daban-daban.

Bayanin ya ce cibiyar kusanto da mazhabobin Musulunci tare da hadin gwiwa da jami'ar mazhabobin Musulunci ne suka shirya gudanar da wannan zaman taro, wanda zai dauki tsawon mako guda ana gudanar da shi.

Daga cikin muhimman abubuwan da taron zai mayar da hankali a kansu akwai nazari kan irin rubuce-rubucen da suka yi a lokacin rayuwarsu, da kuma yadda ya kamata al'ummar musulmi su yi amfa ni da su.

657896




captcha