IQNA

Musulmin Kasar Faransa Sun Kalubalanci Masu Wulakanta Kur'ani

15:03 - September 20, 2010
Lambar Labari: 1997817
Bangaren kasa da kasa; Daruruwan musulmin kasar Faransa ne suka gudanar da wani jerin gwano a birnin Moloz na kasar domin nuna rashin amincewa da wulakanta kur'ani mai tsarki da wasu kiristoci suka yi a kasar Amurka.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na leparisen an bayyana cewa, daruruwan musulmin kasar Faransa ne suka gudanar da wani jerin gwano a birnin Moloz na kasar domin nuna rashin amincewa da wulakanta kur'ani mai tsarki da wasu kiristoci suka yi.

Wadanda suka gudanar da zanga-zangar sun yi tar era taken la'antar makiya addinin Allah da suka kone kur'ani mai tsarki a cikin kasar Amurka da sunan 'yancin bayani ko fadar albarkacin baki, wanda gwamnatin Amurka ba ta iya hana su yin hakan ba.

Da dama daga cikin musulmi mazauna kasashen turai sun matukar damuwa kan irin wannan mataki na rashin adalci da ake nuna musu, domin kawai su musulmi ne.

657925



captcha