IQNA

Musulmin Turkiya Sun Raba Kur'anai Ga Kiristoci Masu Bude Ido

15:04 - September 20, 2010
Lambar Labari: 1997819
Bangaren kasa da kasa; Wasu matasa musulmi a kasar Turkiya sun raba kur'ani mai tsarki ga wasu masu yawon shakatawa da bude ido a kasar, wadanda mabiya addinin kirista ne domin su samu masaniya kana bin da kur'ani ke koyarwa.



Kamfanin dillancin labaran ikna ya habarta cewa a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na milliyat an bayyana cewa, Wasu matasa musulmi a kasar Turkiya sun raba kur'ani mai tsarki ga wasu masu yawon shakatawa da bude ido a kasar, wadanda mabiya addinin kirista ne domin su samu masaniya kana bin da kur'ani ke koyar da dan adam.

Matasan jam'iya sadat ne suka dauki nauyin rarraba kur'anan ga masu yawon shakatawa a kasar daga kasashen yamamcin turai da sauran kasashen duniya wadanda ba musulmi ba, da nufin kara bayyana koyarwar addinin Musulunci.

Musulmin kasar Faransa na daga cikin musulmin duniya da suka nuna rashin amincewarsu da cin zarafin musulmi da aka yi ta hanyar kone kur'ani mai tsarki a Amurka, inda suka yi ta gudanar da zanga-zanga.

657981


captcha