Bangaren kasa da kasa; Za fara gudanar da gasar karatun kur'ani mai tsarki da ta kebanci matasa a kasar Kuwait daga makon gobe, wadda za a kwashe tsawon mako guda ana gudanar da ita a kasar ta Kuwait.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga jaridar Al-anba an bayyana cewa, za fara gudanar da gasar karatun kur'ani mai tsarki da ta kebanci matasa a kasar Kuwait daga makon gobe, wadda za a kwashe tsawon mako guda ana gudanar da ita a kasar.
Ma'ikatar kula da ayyukan addini ta kasar ita ce tare da hadin gwiwa da cibiyar bunkasa harkokin motsa jiki ta matasan kasar suka dauki nauyin wannan gasa, wadda matasa da dama za su halarta.
Wadannan cibiyoyi za su yi amfani da wannan damar wajen wayar da kan matasan, da kuma ba su damar fadada ayyuaknsu na motsa jiki gami da koyon karatu da hardar kur'ani.
657754