Bangaren kasa da kasa; An bude wani taron bayar da horo kan ilmomin kur'ani mai tsarki a birnin Doha na kasar Qatar, wanda cibiyar kula da harkokin kur'ani ta kasar ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa.
Kamfanin dillancin labarn iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga jardar Al-shrq ta kasar Qatar an bayyana cewa, an bude wani taron bayar da horo kan ilmomin kur'ani mai tsarki a birnin Doha na kasar Qatar, wanda cibiyar kula da harkokin kur'ani ta kasar ta dauki nauyin shiryawa.
Babbar manufar gudanar da wannan bayar da horo shi ne kara wayar da kan mata kan ilmomin kur'ani mai tsarki, tare da bas u horo kan ilmomin addini da kuma na zamantakewa daidai da koyarwa irin ta addinin Musulunci.
A cikin shekarar nan dai ma'aikatar kula da harkokin addinin muslunci ta kasar Qatar shirya gudanar da tarukan bayar da horo na addini da dama ga matasa da kuma mata.
657774