IQNA

Taro Kan Fusahar Musulunci A Birnin Doha Na Qatar

10:51 - September 21, 2010
Lambar Labari: 1998319
Bangaren kasa da kasa; Za a gudanar da zaman taro kan fusahar Musulunci na shekara-shekara a birnin Doha na kasar Qatar tare da halartar manyan jami'an gwamnatin kasar da kuma wasu daga cikin kasashen musulmi da na larabawa.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na islamiccartdoha na yanar gizo an habarta cewa, za a gudanar da zaman taro kan fusahar Musulunci na shekara-shekara a birnin Doha na kasar Qatar tare da halartar manyan jami'an gwamnatin kasar da kuma wasu daga cikin kasashen musulmi da na yankin gabas ta tsakiya.

Bayanin ya ci gaba da cewa babbar cibiyar kula da harkokin Musulunci ta sarkin kasar Hamad Bin Khalifa ita ce ta dauki nauyin shirya gudanar da wannan zaman taron, da nufin kara wayar da kan sauran kasashe kan fusahar Musulunci.

Wannan dai shi ne karo na hudu da za a gudanar da wannan zaman taro, wanda zai yi dubi kan muhimman batutuwa da suka danganci cigaban fusahar Musulunci a zamanin da da na yanzu.

658872




captcha