Bangaren kasa da kasa; Rashin yin aiki da da abin da ke cikin kur'ani mai tsarki shi ne babbar musibar da tafi kone kur'ani da aka yi a kasar Amurka, wanda kuma hakan shi ne babban abin da ya jefa msulmi cikin halin suka samu kansu.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin yanar gizo na kamfanin dillancin labaran Iba an habarta cewa, daya daga cikin fitattun malaman jami'ar Azhar ta kasar Masar Muhammad Ashur ya bayyana cewa, rashin yin aiki da da abin da ke cikin kur'ani mai tsarki shi ne babbar musibar da tafi kone kur'ani da aka yi a kasar Amurka, wanda kuma hakan shi ne babban abin da ya jefa musulmi cikin halin suka samu kansu a wannan zamani.
Ya ce Amurkawa da suka kone kur'ani ba su yi imani da shi ba, amma musulmi da ya yi imani da kur'ani da sakon da ke ciki bai yi aiki da shi ba , ya fi muni kan wanda dama bai yarda da shi ba kuma ya wulakanata, domin shi kansa rashin aiki da shi matsayin wlakanta shi ne.
658803