IQNA

Kone Kur'ani Mai Tsarki Tozarta Annabi Isa (AS) Ne

10:50 - September 21, 2010
Lambar Labari: 1998325
Bangaren kasa da kasa; Kone kur'ani mai tsarki wasu kiristoci masu tsattsauran ra'ayi suka yi da kuma bayyana ranar sha daya ga watan satumba ta zama kone kur'ani ta duniya babban cin zarafi ne ga Annabi Isa (AS)



Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa, a wata zantawa da ta hada shi da Musa Abdulmumin masani kuma malamin shi'a a Kosovo ya bayyana cewa, Kone kur'ani mai tsarki wasu kiristoci masu tsattsauran ra'ayi suka yi da kuma bayyana ranar sha daya ga watan satumba ta zama kone kur'ani ta duniya babban cin zarafi ne ga Annabi Isa (AS) da suke raya cewa suna yi masa biyayya ne.

Bayanin ya ci gaba da cewa a cikin kur'ani mai tsarki an ambaci annabi Isa (AS) da maryam (AS) a wurare da dama, wanda hakan ke nuni da cewa wulakanta kur'ani na nunifin wulakanta duk abin da ke cikinsa da hakan ya hada da Annabi Isa da Maryam da aka mabata a ciki, wannan a hankalce kenan.

Balanta addinin kiristanci babu inda ya bayar da dama a wulakanta addinin ko ci masa zarafi, wanda hakan ke tabbatar da cewa abin wadannan mutanen suka yi ya yi hannun riga da addinin kiristanci.

658779










captcha