IQNA

Cibiyoyin Musulunci A Amurka Sun Fara Gudanar Da Zamansu

14:10 - September 21, 2010
Lambar Labari: 1998636
Bangaren kasa da kasa; Cibiyoyin Musulunci na kasar Amurka sun fara gudanar da zamansu a birnin New York da nufin tattauna muhimman batutuwa da suka shafi bunjasa ayyukansua cikin fadin kasar.



Kamfanin dilalncin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na Iraq an bayyana cewa, cibiyoyin Musulunci na kasar Amurka sun fara gudanar da zamansu a birnin New York da nufin tattauna muhimman batutuwa da suka shafi bunjasa ayyukansua cikin fadin kasar ta Iraki.

Bayanin ya ci gaba da cewa wannan taro ya wannan zaman taro da cibiyoyin suke gudanarwa zai mayar da hanakali ne kan matsalolin da musulmi suke fuskanta a halin yanzu a kasashen yammacin turai musamman ma a kasar ta Amurka.

A cikin makonnin da suka gabata ne dai wasu masu tsananin gaba da addinin muslunci da musulmi a kasar ta Amurka suka keta alfarmar alkur'ani mai tsarki.


658708




captcha