IQNA

Keta Alfarmar Kur'ani Mai Tsarki Ya Kara Masa Matsayi A Duniya

14:10 - September 21, 2010
Lambar Labari: 1998637
Bangaren siyasa da zamantakewa; Keta alfarmar kur'ani mai tsarki da wasu tsirarun mutane suka yia kasar Amurka, da kuma yadda ake ci gaba da tsangwamar musulmi da Musulunci a cikin kasashen yammcin turai hakan ya kara masa matsayi na musamman a duniya.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga bangaren yada labarai na cibiyar bunkasa harkokin Musulunci ta Kurdistan an bayyana cewa, shugaban bangaren kula da ayyukan tabligi na cibiyar Ali Khuza'i ya bayyana cewa, keta alfarmar kur'ani mai tsarki da wasu tsirarun mutane suka yia kasar Amurka, da kuma yadda ake ci gaba da tsangwamar musulmi da Musulunci a cikin kasashen yammcin turai hakan ya kara masa matsayi na musamman a duniya baki daya.

Ya ce saboda wawanci da karancin hankali na wadannan mutanen, sun yi zaton cewa kone kur'ani na nufin kawo karshen addinin Musulunci da koyarwar kur'ani a duniya kenan, amma yadda kur'ani ke ci gaba da samun karbuwa da daukakka a duniya, ya tababtar da karancin hankali da tunaninsu.

659038




captcha