Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, jaridar Al-ra'ay ta kasar Kuwait ta habarta cewa, majalisun dokokin kasashen musulmi za su gudanar da zamansu karakshin kungiyar hadin kan kasashen musulmi a birnin Ankara na kasar Turkiya da za a fara gudanarwa a cikin watan nan.
Taron zai samu halartar wasu daga cikin majalisun dokokin kasashen musulmi, inda za su mayar da hankali kan muhimman batutuwa da su ke ci musulmi tuwo a kwarya.
Yanzu haka dai wasu daga cikin 'yan majalisun dokokin kasashen musulmi sun fara isa birnin na Ankara domin halartar taron.
658978