Bangaren siyasa da zamnatakewa, Mataimakin shugaban majalisar mabiya mazhabar shi'a na kasar Labanan Ayatollah Qabalan ya jaddada wajabcin zaman lafiya tsakanin dukkanin mabiya addinai a kasar Labanan.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa a wani bayani da ya nakalto daga bangaren yada labaransa na birnin Beirut cewa, mataimakin shugaban majalisar mabiya mazhabar shi'a na kasar Labanan Ayatollah Qabalan ya jaddada wajabcin zaman lafiya tsakanin dukkanin mabiya addinai a kasar.
Bayanin ya ci gaba da cewa malamin ya bayayana hakan ne sakamakon hankoron da wasu suke yi a kasar na ganin sun haifar da fitina da rashin jituwa tsakanin al'ummar kasar ta Labanan.
Ya ce shekaru masu yawa al'ummar kasar suna zamansu lafiya, amma sakamakon shiga cikin harkokinsu na cikin gida da ake hakan na neman ya mayar da kasar cikin rikici, dole ne a yi hattara.
658954