Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Libya al-yaum an bayyana cewa, An bude gasar kur'ani mai tsarki ta kasa da kasa da aka baiwa lakabin Alfateh a kasar Libya a ranar Litinin da ta gabata a birnin Tripoli babban birnin kasar.
Bayanin ya ci gaba da cewa wannan gasa ana gudanar da irinta a kowace shekara yau tsawon shekaru bakwai a jere a matsayi na kasa da kasa, tare da halartar makaranta daga kasashen duniya daban-daban.
Taron bude gasar ya samu halartar manyan malaman addinin Musulunci na kasa da kuma masana daga jami'oi gami da wakilan cibiyoyin addini da na nazari a kasar.
659571