IQNA

An Girmama Wadanda Suka Shiga Gasar Nakasassu Ta Masar

15:07 - September 22, 2010
Lambar Labari: 1999547
Bangaren kasa da kasa; An girmama wadanda suka shiga gasar nakasassu ta kur'ani mai tsarki a kasar Masar, musamamn ma wadanda suke matsalar tabuwar hankali daga cikinsu.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakakto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar kasar Masar ta Yaum sabi an bayyana cewa, an girmama wadanda suka shiga gasar nakasassu ta kur'ani mai tsarki a kasar Masar, musamamn ma wadanda suke matsalar tabuwar hankali daga cikin wadanda suka shiga gasar.

Bayanin ya ci gaba da cewa gidan talabijin Azhari da ke watsa shirye-shiryensa kan tauraroron dan shi ne ya dauki nauyin watsa gasar da kuma taron girmamam wadanda suka shiga gasar kai tsaye.

A yayin gudanar da taron an gabatar da jawabai da ke nuni da cewa wadanda ake ganin suna da matsalloli a cikin al'umma su ma suna da rawar da za su takawa gwargwardon ikon da suke da shi.

659558









captcha