IQNA

Ana Ci Gaba Da Nuna Rashin Amincewa Da Wulakanta Kur'ani A Turkiya

17:30 - September 22, 2010
Lambar Labari: 1999674
Bangaren kasa da kasa; Ana ci gaba da nuna rashin amincewa da keta alfarmar kur'ani mai tsarki a kasar Turkiya, tun bayan da wasu 'yan tsirarun kiristoci masu tsattsauran ra'ayi suka kone kur'ani mai tsarki a kasar Amurka.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga wani shafin sadarwa na yanar gizo a kasar Turkiya an habarta cewa, ana ci gaba da nuna rashin amincewa da keta alfarmar kur'ani mai tsarki a kasar Turkiya, tun bayan da wasu 'yan tsirarun kiristoci masu tsattsauran ra'ayi suka kone kur'ani mai tsarki a kasar Amurka da nufin tsokanar musulmi.

Bayanin ya kara da cewa musulmi a garuruwan kasar Turkiya suna gudanar da gangami da nufin tabbatar wa duniya cewa ba su amince da keta alfarmar kur'ani ba, kuma a shirye suke su sadaukantar da rayukansu domin kare kur'ani.

Musulmin Turkiya suna gudanar da taruka da gangami a wasu garuruwan ma hard a zanga-zanga, inda suke yin Allawadai da cin zarafin musulmi da ake yi a kasashen da ke raya cewa suna kare hakkin dan adam.

659618




captcha