IQNA

An Zabi Sabon Shugaban Majalisar Musulmin Kasar Jamus

17:30 - September 22, 2010
Lambar Labari: 1999675
Bangaren kasa da kasa; An zabi shugaban majalisar musulmin kasar Jamus, a matsayin sabon shugaban da zai jagoran ragamar tafiyar da harkokin musulmin kasar karkashin wannan majalisa.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na Muhit an bayyana cewa, An zabi shugaban majalisar musulmin kasar Jamus, a matsayin sabon shugaban da zai jagoran ragamar tafiyar da harkokin musulmin kasar karkashin wannan majalisa ta musulmin kasar.

Rahoton ya ce wannan bayani ya zo a cikin wata sanarwa da majalisar ta fitar, inda aka bayyana cewa Aiman Mazik shi ne wanda mambobin majalisar suka zaba ya zama sabon shugaban majalisar bayan zaben da aka gudanar.

Majalisar musulmin kasar Jamus dai tana da manyan mambobi goma sha biyar, tara daga cikinsu sun kada wa Aiman Mazik kuri'a, yayin da shida daga cikinsu bas u zabe shi ba.

659646



captcha