Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya zuwa yanzu kimanin mutane 250 daga cikin masu fasahar zayyanar kur'ani suka bayyana cewa a za su halarci taron fasahar rubutun kur'ani na kasa da kasa da za a gudanar a birnin Madina mai alfarma da za a gudanar kasa makonni uku masu zuwa.
Shugaban kwamitin shirya gudanar da zaman taron Muhammad salim Al-aufi ya bayyana cewa, an bayar da sanarwar cewa dukkanin masu sha'awar shiga cikin taron za su iya yin rijistar sunayensu.
Ya ce yanzu haka dai adadin mutanen da suka yi rijistar shiga taron domin nuna fasahar da Allah ya ba su a wanna fage sun kai 250, daga kasashe 31 na musulmi.
659651