IQNA

Musulmin Amurka Za Su Gudanar Da Tarukan Musulunci

17:30 - September 22, 2010
Lambar Labari: 1999677
Bangaren kasa da kasa; Kungiyoyin musulmin kasar Amurka za su gudanar da taruka kan matsayin Musulunci da kuma wuraren ibada, da aka yi wa lakabi da ranar bude kofofin masallatai, wanda za a gudanar nan da makonni hudu masu zuwa.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na haberroku cewa, kungiyoyin musulmin kasar Amurka za su gudanar da taruka kan matsayin Musulunci da kuma wuraren ibada, da aka yi wa lakabi da ranar bude kofofin masallatai, wanda za a gudanar nan da makonni hudu masu zuwa a nan gaba.

Kungiyoyin musulmin kasar Amurka sun kudiri aniyar gudanar da wannan taron ne da nufin mayar da martani ta hanyar da ta dace ga masu nuna tsananin kiyayya ga addinin muslunci da kuma musulmi a kasar ta Amurka.

Wani jin ra'ayin jama'a da aka gudanar a kasar Amurka ya tabbatar da cewa mafi yawan Amurkawa bas u da masaniya kan addinin Musulunci, wannan ne babban dalilin da ya sanya suke fadawa cikin tarkon yahudawa.

659796






captcha