Kamfanin dillancin labaran kur'ani iqna ya habarta cewa, a wani bayani da ya nakalto daga shafin yanar gizo na ISESCO an habarta cewa, za a gudanar da wani zaman taro a Ireland da zai yi dubi kan yadda kyamar Musulunci ke ci gaba da karuwa a cikin kasashen turai.
Rahoton ya ce kungiyar kula da bunkasa harkokin al'adu da ilimi ta ISESCO ita ce ta dauki nauyin shirya wannan zaman taro, wanda zai dubi kan wannan matsala da kuma tattauna hanyoyin warware ta.
Matsalar kyamar addinin musuluci a cikin kasashen turai na daga cikin muhimman abubuwan da musulmi suke kokawa a kansu a wannan zamani.
660467