Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa a wani rahoto da ya nakalto daga shafin yanar gizo na kungiyar hadin kan kasashen musulmi an bayyana cewa, babban sakataren kungiyar kasashen musulmi Abdulaziz Usman Altuwaijari ya gabatar da wani jawabi a jami'ar Dobrik ta kasar Crotia da ke gabacin nahiyar turai.
Tuwaijari ya gabatar da jawabin nasa a gaban daruruwan malamai da daliban jami'ar, dangane muhimman ayyukan da ya kamata masana su mayar da hankali kansu na kusanto da fahimtar juna tsakanin al'adu.
A cikin jawabin nasa ya jaddada muhimmancin samar da hanyar tattaunawa mai zaman kanta tsakanin addinai da al'adu na duniya baki daya da nufin karfafa danganta tsakaninsu.
660518